MDD : Kwamitin Sulhu ya yi tir da kisan ‘Yan Alawiyya A Siriya

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi Allah wadai da kisan kiyashin da aka yi a baya-bayan nan a yammacin Syria, inda ya yi

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi Allah wadai da kisan kiyashin da aka yi a baya-bayan nan a yammacin Syria, inda ya yi kira ga hukumomin rikon kwarya a kasar, da su kare “dukkan ‘yan Syria ba tare da nuna bambanci ba,” ba tare da la’akari da kabila, addini ba.

Majalisar ta yi kakkausar suka kan tashe-tashen hankulan da ke faruwa a lardunan Latakia da Tartus tun daga ranar 6 ga Maris, ciki har da kisan kiyashin da aka yi wa fararen hula, musamman a cikin al’ummar Alawite, ‘yan tsirarun da ke da alaka da dangin tsohon shugaban kasar Bashar al-Assad.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments