MDD : Kwamitin Sulhu ya yi tir da kisan ‘Yan Alawiyya A Siriya

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi Allah wadai da kisan kiyashin da aka yi a baya-bayan nan a yammacin Syria, inda ya yi kira ga hukumomin rikon kwarya a kasar, da su kare “dukkan ‘yan Syria ba tare da nuna bambanci ba,” ba tare da la’akari da kabila, addini ba. Majalisar ta yi […]
Iran ta yi kakkausar suka kan sabon takunkumin Amurka

Iran ta yi kakkausar suka kan sabon takunkumin da Amurka ta kakabawa Ministan Man Fetur na aksar Mohsen Paknejad da wasu hukumomi da jiragen ruwa masu ruwa da tsaki a harkar danyen man fetur da kasar ke fitarwa, tana mai cewa matakin keta doka da munafunci ne daga bangaren Amurka. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar […]
Dubban Musulmi Sun Yi Sallar Juma’a A Masallacin Kudus Duk Da Barazanar Isra’ila

Dubun dubatar musulmi masu ibada ne suka gudanar da sallar Juma’a ta biyu na watan Ramadan a harabar masallacin Al-Aqsa, duk da tsauraran matakan da Isra’ila ta dauka na hana Falasdinawa shiga wurin mai tsarki. Sashen kula da masallacin da ke birnin al-Quds ya ce kimanin masu ibada 80,000 ne suka taru A daidai lokacin […]
Karancin Man Fetur A Jamhuriyar Nijar Yana Damun ‘Yan Kasa

An kusa shiga mako guda daga lokacin da aka fara fuskantar karancin mai a gidajen man fetur da hakan ya jefa masu ababan hawa cikin damuwa. Rabon man fetur da kamfanin SONIDEP yake yi bai wadatar da masu abubuwan hawa ba, yana kuma kawo cikas a harkokinsu na yau da kullum. Da akwai dalilai da […]
An Yi Gargadi Akan Rushewar Kungiyar Agajin Falasdianwa Ta UNRWA

Shugaban kungiyar agajin Falasdinawa ta “UNRWA’ wacce MDD ta kafa, ya yi gargadin rushewarta da hakan zai hana Falasdinawa na yanzu samun ilimi, haka nan kuma bayar da kayan agaji da bukatun yau da kullum ga mutane miliyan 6 a Falasdinu. Shugaban kungiyar Agajin Philippe Lazzarini ya fada wa kamfanin dillancin labarun Faransa cewa; Da […]
HKI Tana Cigaba Da Keta Tsagaita Wutar Yaki A Lebanon

A jiya Alhamis sojojin HKI sun cigaba da keta aiki da kuduri mai lamba 1701 ta hanyar yin shawagi a samaniyar Lebanon da kuma kai hare-hare a yankunan Jenta da Biqa. Tashar talabijin din ‘almanar ta watsa labarin da yake cewa; Jiragen yakin abokan gaba ‘yan sahayoniya sun kai hare-hare har sau uku a yankin […]
Taron Kasashen Iran, Rasha Da China A Birnin Beijing Ya Bukaci A Kawo Karshen Takunkumai Akan Tehran

A yau Juma’a ne aka bude taron kasashen Iran, Rasha da China, a matakin mataimakan ministocin harkokin waje inda su ka tattauna shirin makamashin Nukiliya na Iran. Mahalarta taron sun bukaci ganin an dauke wa Iran takunkuman da aka kakaba mata, sannan kuma a warware batun shirinta na makamashin Nukiliya ta hanyar tattaunawa. Kasashen na […]
Araqchi: Iran ta karbi Wasikar Trump kuma tana yin nazari a kanta

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya ce ya karbi wata wasika daga shugaban kasar Amurka Donald Trump ta hannun manzon kasar Hadaddiyar Daular Larabawa. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Araghchi ya bayyana cewa, na karbi bakuncin Anwar Gargash mai baiwa shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa shawara kan harkokin […]
Rasha ta caccaki sabbin mahukuntan Syria kan kisan tsiraru

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, a wani taron sirri da kwamitin sulhu na MDD ya yi a wannan mako kasar Rasha ta yi Allah-wadai da sabuwar gwamnatin kasar ta Syria dangane da kisan kiyashin da jami’anta suke yi a kan tsiraru a kasar. Wannan dai na zuwa ne bayan da kungiyar […]
Senegal ta yi Allah-wadai da tsare ‘yan kasarta a Mauritania

Ministar Harkokin Wajen Senegal, Yacine Fall, ta ce hukumomin kasarta sun bayyana rashin jin dadi game da tsare ‘yan Senegal da kuma tilasta musu barin kasar bisa zarginsu da zama cikin Mauritania ba bisa ka’ida ba. Hukumomin kasar Mauritaniya sun kaddamar da wani gangamin korar bakin haure daga kasashen Afirka daban-daban. A wani jawabi da […]
Somalia: Adadin wadanda suka mutu a harin Al-Shabaab ya haura 10

Adadin wadanda suka mutu sakamakon harin da kungiyar al-Shabaab ta kai a wani otel da ke garin Baledweyne, inda shugabannin kabilu ke ganawa ya kai mutane 10, kamar dai yadda majiyoyin ‘yan sanda na kasar ta Somalia suka tabbatar. Sannan kuma bayanin hukumar ‘yan sandan ta kasar Somalia ya tabbatar da cewa, akasarin wadanda suka […]