MDD : Dole Ne Poland Ta Kama Netanyahu Idan Ya Sanya Kafa Kasar

Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman Francesca Albanese ta yi kira ga Poland da ta mutunta ka’idojin duniya ta hanyar kame firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu

Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman Francesca Albanese ta yi kira ga Poland da ta mutunta ka’idojin duniya ta hanyar kame firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu idan ya sanya kafa kasar.

Kalaman na Albanese wani martani ne ga kasar Poland da tun farko ta yi Allah wadai da kasar Mongoliya saboda gazawarta na cafke shugaban kasar Rasha Vladimir Putin bisa sammacin kama shi daga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC.

“Ana bukatar membobin ICC su kama mutanen da ke karkashin sammacin ICC,” kamar Albanese ta rubuta.

A yammacin ranar Juma’a ne aka gudanar da zanga-zanga a birnin Warsaw na kasar Poland domin nuna adawa da sanarwar da gwamnatin kasar ta bayar na cewa za ta yi watsi da sammacin kama Benjamin Netanyahu idan ya ziyarci kasar a wannan watan.

A watan Nuwamban 2024 ne, Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta ba da sammacin kama Netanyahu da tsohon ministansa na soja Yoav Gallant, wadanda ake zargi da laifukan yaki da cin zarafin bil adama a Gaza.

Yawancin kasashen Turai sun sanar da cewa zasu mutunta hukuncin kotun kuma suna iya daukar matakan da suka dace don aiwatar da shi.

Sai dai Amurka ta yi watsi da hukuncin kotun ta Hague tana mai cewa kotun ba ta da hurumin sauraren karar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments