MDD: Babu Wani Wuri Mai Aminci A Gaza

A cigaba da nuna damuwa akan halin da yankin Gaza yake ciki, MDD ta yi gargadi akan cewa babu wani wuri da ya saura mai

A cigaba da nuna damuwa akan halin da yankin Gaza yake ciki, MDD ta yi gargadi akan cewa babu wani wuri da ya saura mai aminci a cikin wannan yankin, don haka ya zama wajibi a tsagaita wutar yaki a cikin gaggawa ba tare da bata lokaci ba.

Kamfanin dillancin labaru “Tasnim’ ya nakalto jami’ar MDD mai kula da harkokin jin kai tana cewa; “Yan’adamtaka tana cikin hatsari, domin ya zuwa yanzu mutanen da su ka yi shahada sun haura 41,000.

Bugu da kari jami’ar ta MDD Sigrid Agnes Maria Kaag ta yi ishara da rahoton bayan nan na MDD wanda yake nuni da cewa fiye da mutane 22,000 ne su ka jikkata, kuma a cikinsu da akwai wani adadi dake tsakanin 13,000 zuwa 17,000 wadanda sun rasa gabobinsu.

Bugu da kari rahoton ya ce da akwai wani adadi mai yawa na wadanda su ka jikkata wadanda suke fama da rubewar wani sashe na jikinsu saboda rashin magani da kayan aiki a asibitoci.

Shi kuwa jakadan kasar Rasha a MDD Vasily Nebenzya ya bayyana  cewa rashin tsagaita wuta a Gaza yana nufin cewa dukurorin MDD akan Gaza sun zama rubutu akan takarda kawai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments