MDD : akwai kyakyawan fata na samun ci gaba a Afirka a 2026

Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da rahotonta na shekara-shekara kan yanayin tattalin arzikin duniya. Rahoton ya yi hasashen dan karuwar ci gaba a 2026, saidai

Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da rahotonta na shekara-shekara kan yanayin tattalin arzikin duniya.

Rahoton ya yi hasashen dan karuwar ci gaba a 2026, saidai har yanzu bai isa a cimma burin da aka sa gaba ba.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasashen cewa Afirka za ta samu ci gaba da kashi 4.1% a shekarar 2026, dan karamin ci gaba idan aka kwatanta da kashi 3.9% na shekarar da ta gabata.

Gabashin Afirka,shi ne cibiyar tattalin arzikin nahiyar, in ji Stephen Karingi, Darakta a Hukumar Tattalin Arziki ta Afirka.

Kyakkyawan misali shi ne cinikin wutar lantarki,” in ji shi.

A cewar Bankin Duniya, talauci a Afirka da ke kudu da hamadar Sahara ya kai kashi 43%.

“Afirka ba za ta iya dogara da taimakon ci gaba na hukuma ba.” Domin cimma wannan burin, inji Stephen Karingi, Darakta a Hukumar Tattalin Arziki ta Afirka, yana dogaro da jarin Afirka, maimakon taimakon Ć™asashen duniya.

Kafin Shugaba Donald Trump ya dakatar da shi shekara guda da ta gabata, tallafin da Amurka ke bai wa ƙasashen kudu da hamadar Sahara ya kai dala biliyan 11.5.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted