“Yan Sandan Habasha Sun Kama Mutane 22 Masu Alaka Da Fataucin Mutane

Jami’an ‘yan sandan kasar Habasha sun kama  wasu mutane 22 da suke da alaka da fataucin mutane kusan 2,000 wadanda kuma su ka haddasa mutuwar mutane biyu. Sanarwar da ‘yan sandan kasar ta Habasha su ka fitar ta kuma ce,mutanen da aka kama suna a cikin wata kungiya ce mai samun miliyoyin kudade ta hanyar […]

 Arakci: Babu Tattaunawa Da Amurka A Karkashin Barazana

ministan harkokin wajen Iran

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci  ya fada a yau Laraba cewa; Duk wata tattaunawar diplomasiyya a karkashin barazar soja, ba za ta haifar da Da,mai ido ba, yana mai kara da cewa; Tattaunawa da Amurka ya kamata ta zama an yi ta ne  bisa girmama juna nesa da shifta da kuma barazana ta soja.” […]

Iran ta yi watsi da rahotannin cewa an kashe masu zanga zanga 30,000

Iran ta musanta rahotannin dake cewa an kashe mutum kimanin 30, 000 a yayin zanga zangar lumanr data rikide zuwa tarzoma a kasar kwanan nan. Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya mayar da martani a cikin wani sako, game da abin da ya kira karyar kafofin watsa labarai game da abubuwan da […]

Iran ta yi gargadi mai tsanani kan barazanar soja daga Trump

Iran ta yi gargadi a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya game da barazanar da Amurka ta yi wa Tehran a bayyane. Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saeed Iravani, ya ce kalaman barazana na Washington ba su takaita ga Iran kawai ba, yana mai tabbatar da cewa Amurka tana ci gaba da […]

Turkiyya da Najeriya sun karfafa alaka a fannoni da dama

Shugaba Erdogan na Turkiyya da takwaransa na Najeriya Bola Tinubu sun jagoranci sanya hannu kan yarjeniyoyi da dama a tsakanin kasashen biyu. Matakin ya shafi zurfafa hadin gwiwa a fannoni daban-daban na masana’antu, kasuwanci, zuba jari, tsaro da dai saurensu. An sanya hannu kan yarjejeniyoyi tara jimilla a gaban Shugaba Recep Tayyip Erdogan da Tinubu […]

MDD : akwai kyakyawan fata na samun ci gaba a Afirka a 2026

Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da rahotonta na shekara-shekara kan yanayin tattalin arzikin duniya. Rahoton ya yi hasashen dan karuwar ci gaba a 2026, saidai har yanzu bai isa a cimma burin da aka sa gaba ba. Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasashen cewa Afirka za ta samu ci gaba da kashi 4.1% a shekarar […]

 Sama Da Mutane Miliyan 3 Da Yaki Ya Daidaita A Sudan Ne Suka Koma Gida

Hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar dinkin Duniya ta ce sama da mutane miliyan 3 da yakin da aka shafe kusan shekaru 3 ana gwabzawa a Sudan ne suka koma gidajensu, duk da yadda ake ci gaba da fuskantar mummunan rikici a sassan kasar. A cikin wani rahoto da ta fitar , Hukumar […]

Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa 4 A Wani Harin Da Ta kai A Yankin Gaza

A wasu sabbin hare-hare da isra’ila ta kai ta kashe falasdinawa guda 4 da kuma jikkata wasu na daban a yankin gaza a ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da take yi da aka cimma tsakaninsu da kungiyar Hamas da Amurka ta jagoranta. majiyar labaran yankin falasdinu ta bayyana cewa wani yaro […]

Amurka Tana Amfani Da Yakin Kwakwalwa Domin Kawo Tarnaki Ga Batun Tsaron Yankin

shugaban kasar iran Masud Pezeshkiyan yayi gargadin cewa motsin dakarun sojin Amurka a yankin yammacin Asiya wani bangaren ne na kokarin da Amurka keyi na yamutsa batun tsaro a yankin yammancin Asiya shugaban yayi wannan tsoka ci ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da yayi da yarima mai jiran gado na kasar Saudiya mohammad […]