MDD : Aikinmu A Gaza Na Cikin Tsaka Mai Wuya

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa aikin da take yi na isar da kayan agaji ga al’ummar Gaza na cikin tsaka mai wuya, sakamakon

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa aikin da take yi na isar da kayan agaji ga al’ummar Gaza na cikin tsaka mai wuya, sakamakon abin da ta ta kira ayyukan zagon kasa da sojojin Isra’ila da ƴan daban Falasdinawa ke gudanarwa.

Sakataren MDD mai kula da harkokin jin kai Tom Fletcher, ya zargi sojojin Isra’ila da kai hari a kan ayarin motocin Majalisar Dinkin Duniya a tsakiyar Gaza tare da kai farmaki kan wani sanannen wurin rarraba abinci.

Mista Fletcher ya yi kira ga mambobin Majalisar Dinkin Duniya da su dage kan kare dukkan ayyukan jin kai.

Haka kuma MDD, ta hanyar Ofishinta na kula da ayyukan jin kai OCHA ta nuna matukar damuwa kan rahotannin da ke cewa wani jariri dan wata daya ya mutu sakamakon sanyi a zirin Gaza, a cewar ma’aikatar lafiya ta kasar.

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya shaida wa taron manema labarai cewa, wannan shi ne karo na takwas da wani yaro ya mutu sakamakon sanyi cikin kasa da makonni uku, kuma duk wannan silansa shi ne rashin isar da kayan agajin da ake bukata a zirin ne.

A wani labarin kuma adadin Falasdinawan da Isra’ila ta kashe sun kai akalla 45,885 tare da raunata wasu 109,196 a Gaza tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023, a cewar ma’aikatar lafiya ta yankin da ke kewaye.

Akalla mutane 31 aka kashe a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, in ji sanarwar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments