Mayakan Kungiyar Ta’addanci Ta ISIS Sun Sake Kunno Kai A Garuruwan Deir ez-Zor Da Hasaka Na Siriya

Mayakan kungiyar ta’addanci ta ISIS sun sake kunno kai a garuruwan Deir ez-Zor da Hasaka na kasar Siriya Yankunan Deir ez-Zor da Hasakah dake arewa

Mayakan kungiyar ta’addanci ta ISIS sun sake kunno kai a garuruwan Deir ez-Zor da Hasaka na kasar Siriya

Yankunan Deir ez-Zor da Hasakah dake arewa maso gabashin kasar Siriya suna ci gaba da samun karuwar bullar ayyukan ta’addancin kungiyar ISIS tun daga farkon wannan wata. Hare-hare 13 sun kai sune kan Dakarun Syrian Democratic Foeces ta (SDF) ta Kurdawa masu samun goyon bayan Amurka da kuma fararen hulan yankunan, lamarin da ya janyo hasarar rayuka.

A cewar kungiyar kare hakkin bil- adama ta Syria, hare-haren sun bambanta wajen aiwatar da su, daga harin kwanton bauna zuwa na kai hari kai tsaye, wanda ke nuni da yadda kungiyar ta canza yanayin kai hare-hare a yankunan saboda matakan tsaron a garuruwan. Wadannan al’amura sun kuma nuna cewa kungiyar ta’addancin na ci gaba da yin barazana a arewaci da gabashin Siriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments