Search
Close this search box.

Mayakan Boko Haram Sun Kashe Manoma Da Dama A Gonakinsu A Jihar Yobe

Mayakan kungiyar yan ta’adda ta boko haram sun kashe manoma kauyawa a garin Wafa na karamar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe na tarayyar Najeriya. Jaridar

Mayakan kungiyar yan ta’adda ta boko haram sun kashe manoma kauyawa a garin Wafa na karamar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe na tarayyar Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa, jami’an tsaro sun tabbatar da aukuwar haka amma basu bayyana adadin wadanda aka kashe ba.

Har’ila yau Jaridar ta tabbatar da cewa hare haren sun auku ne da misalign karfi 4 na yamma a lokacinda kauyawan suka kammala ayyukansu na gona suna dawowa gida. Har’ila yau yan ta’addan sun kona gidaje da dama a kauyen.

Labarin ya kara da cewa a cikin watan da ya gabata kadai yan ta’addan sun kashe mutane biyu, sannan sun kona gidaje kimani 475 wanda ya tilastawa mutane 2,390 yin hijira daga yankin.

Wani wanda ya ganewa idanunsa ya bayyana cewa mai yuwa yan ta’addan sun dau fansa ne a kansu, sabosa bawa jami’an tsaro labaran asiri dangane da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments