Indonesiya da Koriya ta Kudu na shirin yin watsi da dala a harkokinsu na kasuwanci

Kamfanin dillancin labaran Parstoday ya bayar da rahoton cewa, Indonesia da Koriya ta Kudu sun amince da wani tsarin hadin gwiwa na aiwatar da hada-hadar kudin gida (LCT) tsakanin kasashen biyu da nufin inganta amfani da kudin Rupiah na Indonesia da kuma na Koriya ta Kudu, a cinikayyar kasashen biyu. A cikin wani rahoto da […]

Isra’ila Ta Bude Sabon Fagen Fama A Yankin Yamma Da Kogin Jordan

Gwamnatin HKI tana son budewa kanta wata jahannama a yankin yamma da kogin Jordan bayan da fara yaki gadan-gadan da kungiyoyin falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan musamman a sansanin yan gudun hjira ta Jenin. A cikin yan kwanakin da suka gabata ne sojojin HKI suka kai wasu hare hare na musamman a wasu […]

Mayakan Boko Haram Sun Kashe Manoma Da Dama A Gonakinsu A Jihar Yobe

Mayakan kungiyar yan ta’adda ta boko haram sun kashe manoma kauyawa a garin Wafa na karamar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe na tarayyar Najeriya. Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa, jami’an tsaro sun tabbatar da aukuwar haka amma basu bayyana adadin wadanda aka kashe ba. Har’ila yau Jaridar ta tabbatar da cewa hare […]

Iran Da Rasha Na Daf Da Kammala Cikakkiyar Yarjejeniyar Dake Tsakaninsu_Lavrov

Kasashen Iran da kuma Rasha zasu kamala cikakiyar yarjejeniyar dake a tsakaninsu nan ba da jimawa ba. Wannan bayyanin ya fito ne ta bakin ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov wanda ya ce Rasha za ta kammala cikakkiyar yarjejeniya tsakaninta da Iran “nan gaba kadan.” Lavrov ya ce kasashen biyu “za su kulla sabuwar yarjejeniya […]

Birtaniya Ta Dakatar Da Sayar Wa Isra’ila Wasu Makamai

Gwamnatin Birtaniya ta sanar da cewa kasar ta dakatar da sayar wa Isra’ila wasu makamai. Matakin ya zo ne bayan kammala wani bincike kan ko Isra’ila na bin dokar kasashen duniya kan tausaya wa dan’adam yayin yakin da take yi a Gaza, inji sakataren harkokin wajen Birtaniyar David Lammy. Lammy, ya ce an dakatar da […]

IAEA : Grossi Na Fatan Farfado Da Yarjejeniyar Nukiliyar Iran

Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ya bayyana fatansa na ganin an farfado da yarjejeniyar nukuliyar Iran. Rafael Grossi, ya yi wanan tsokacin ne a matsayin amsa ga bukatar sabon shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, wanda son a sabunta tattaunawa da nufin samun fahimtar juna game da shirin nukiliyar Iran na […]

UNRWA : Kashi 70 Cikin 100 Na Makarantun MDD A Gaza Sun Lalace

Shugaban hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinu ya ce kashi 70 cikin 100 na makarantun UNRWA ‘sun lalace tun bayan da gwamnatin Isra’ila ta kaddamar da yakin da take yi a yankin da akayi wa kawanta. Philippe Lazzarini, kwamishinan janar na UNRWA ya rubuta a cikin wata sanarwa a ranar […]

Najeriya : Kotu Ta Aika Masu Zanga-zangar Kin Jinin Gwamnati Gidan Yari

Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta aika da mutum 10 wadanda ake zargi da hannu a zanga-zangar kin jinin gwamnati zuwa gidan yari. Mai shari’a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya ya aika da maza tara gidan gyaran hali na Kuje sannan ya aika da mace daya zuwa gidan yarin Suleja. Haka kuma alkalin ya […]