Gwamnatin Amurka ta ƙi ba wa shugaban Majalisar Gudanar da Mulkin Soji a Suadan biza don halartar Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya saboda kin amincewa da shawarar tsagaita wuta, wanda hakan ke nuna girman rashin jituwar da ke tsakanin ɓangarorin biyu
Ƙoƙarin Amurka na tilastawa bangarorin da suke rikici da juna a Sudan yana fuskantar wani ƙalubale a ci gaba da musayar hare-hare tsakanin sojojin Sudan da Rundunar Kai Daukin Gaggawa ta (Rapid Support Forces). An zargi kungiyar Rapid Support Forces da ƙaddamar da hare-haren jiragen sama marasa matuƙa ciki a karo na biyu kan wuraren soji da fararen hula a birnin El Obeid.
A halin yanzu, rundunar sojin Sudan ta bayyana cewa tana samun nasarori a yankuna da dama na Kordofan da Darfur. Duk da haka, ƙwararru suna zargin Amurka da goyon bayan kungiyar Rapid Support Forces da kuma ƙara tsaurara takunkumi kan gwamnatin Sudan ba tare da bayar da wani kwarin gwiwa ba wanda zai iya ƙarfafa sojojin su amince da tsagaita wuta na ɗan lokaci.