An Gudanar Da Tarukan Makoki Shahadar Imam Ridha (AS) A Hubbarensa Da Ke Mashhad

A dai dai ranar da ake juyayin shahadar limami na 8 daga cikin limaman shia miliyoyin mutane daga ciki da wajen kasar Iran sun yi

A dai dai ranar da ake juyayin shahadar limami na 8 daga cikin limaman shia miliyoyin mutane daga ciki da wajen kasar Iran sun yi cincirindo a hubbaren sa da ke birnin Mashahd na arewa maso gabacin kasar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewam juyayin da mabiya mazahabar iyalan gidan manzon All..(s) suke yi a ko wace shekara ya sami taron mutanen daga dukkan fadin kasar Iran da kuma wasu kasashen waje. Inda masu karatun makoki suka bayyana yadda Limamin ya ya shahada a hannun sarki Ma’amun daya daga cikin sarakunan ambasiyya a sekara ta 203 H.K.

Sannan an gabatar da wakoki na juyayi ta hanyoyin nuna bakin ciki da shahadarsa da dama.

Banda haka wasu kuma sukan dauki nauyin abinci da abin shan masu ziyara don raya wannan rana daga cikin ranakun All..ta’aka.

 

 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted