Masu gwagwarmaya a kasar Iraki sun bada sanarwan kai hare hare kan wurare masu muhimmanci a birnin Umm-RashRash na kasar Falasdinu da aka mamaye.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran tanakalto majiyar dakarun na kasar Iraki na cewa sun cilla makamai masu linzami kan sansanin sojojin HKI dake Umm-Rashrash ko (Eilat) na bakin tekun Akaba a safiyar yau Laraba. Inda makaman suka yi barna mai yawa.
Labarin ya kara da cewa dakarun sun kai hare haren ne don tallafawa al-ummar falasdinu wadanda sojojin HKi suke kashewa tun ranar 7 ga watan Octoban shekarar da ta gabata. Sannan sun kara da cewa zasu ci gaba da kai hare hare har zuwa lokacinda za’a dakatar da yaki a Gaza.
Ya zuwa yanzu dai sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa kimani 41 a gaza watanni kimani 11 da suka gabata. Banda haka sun rauna wasu kimani dubu 92. Labarin ya kara da cewa mafi yawan wadanda abin ya shafa mata da yara ne.