Masar Ta Bukaci Warware Rikicin Habasha Ta Hanyar Tattaunawa

kasar masar ta bukaci a warware rikicin habasha ta hanyar tattaunawa mai makon yaki

Shugaba Abdel Fattah al-Sisi na Masar ya bukaci a koma  teburin tattaunawa don sulhunta rikicin Habasha maimakon tunkarar matsalar ta fuskar yaki, yana mai cewa ta haka ne kawai za a warware matsalar wadda ake fargabar za ta iya fantsama zuwa kasashen makwabta

Shugaba al-Sisi wanda ya karbi bakoncin taron tsakiyar shekara na kungiyar Tarayyar Afrika da ya gudana a jiya Lahadi a birnin El-Alamein na gaɓar tekun mediterraniya, taron da ya taɓo matsalolin da suka dabaibaye nahiyar ta Afrika, kodayake ya fi mayar da hankali kan yaƙin da ke faruwa yanzu haka a Habasha tsakanin dakarun gwamnati da mayaƙan ƴantawayen Tigray na TPLF.

A gefen taron na AU, al-Sisi ya yi amfani da damar wajen ganawa ta musamman da takwarorinsa na ƙasashen Eritrea da Somalia da kuma Sudan waɗanda dukkaninsu ke zaman doya da manja da Habashan, inda suka tattauna kan yadda zasu tunƙari matsalar yaƙin na maƙwabciyarsu tare da ɗaukar matakan kaucewa ganin yaƙin ya faɗaɗa musamman a yankunan kan iyaka.

Shugaban na Masar wanda na sahun ƙasashe 4 da Habasha ta zarga da taimakawa ƴan tawayen Tigray, ya ce matsalolin kan iyaka na buƙatar haɗa hannun ƙasashen wajen tunƙararsu ba tare da tunani wani tsagi na tunzura wani ba, kalaman da kai tsaye ke matsayin martani ga Habasha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted