Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdelatty da takwaransa na Rasha Sergey Lavrov sun yi tattaunawa ta wayar tarho game da batun halin da ake ciki a yankin, inda suka mayar da hankali kan batun tsagaita wuta a Gaza da kuma yakin da ake yi a Sudan.
A cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Masar ta fitar a ranar Asabar, Abdelatty ya yi nazari kan ci gaba da kokarin da Masar ke yi na karfafa yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da kuma tabbatar da aiwatar da tanade-tanaden da yarjejeniyar ta kunsa.
Ya jaddada muhimmancin ci gaba da aiwatar da wannan yarjejeniya zuwa mataki na biyu na shirin tsagaita wuta, wanda zai magance matsalolin siyasa da ayyukan jin kai domin samun zaman laifiya da kwanciyar hankali mai dorewa a yankin.
Jami’in diflomasiyyar Masar ya kuma tattauna shirye-shiryen taron kasa da kasa da nufin tallafawa sake gina Gaza. Ya jaddada bukatar samar da tallafin duniya don sake gina yankin da ya lalace, da kuma rage wahalhalun da yakin ya haifar.
Ministan harkokin wajen Masar ya ce aiwatar da shirin sake gina yankin Gaza zai dauki tsawon shekaru biyar bisa tsarin da Kungiyar Kasashen Larabawa da Kungiyar Hadin Kan Musulunci (OIC) suka amince da shi, wanda zai lakume kudi da zasu kai dala biliyan 53.
A halin yanzu, Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa kudin da za a kashe wajen farfado da Gaza zai kai kimanin dala biliyan 70.