Masana: Murkushe ‘Yan Gwagwarmayar Falasdinu Ba Zai Hana Yahudawa Aiwatar Da A Jandarsu Ba

Masana sun ce: Murkushe ‘yan gwagwarmaya a birnin Jenin na Falasdinu ba zai hana Isra’ila aiwatar da munanan manufofinta kan yankin gabar yammacin kogin Jordan

Masana sun ce: Murkushe ‘yan gwagwarmaya a birnin Jenin na Falasdinu ba zai hana Isra’ila aiwatar da munanan manufofinta kan yankin gabar yammacin kogin Jordan ba

Masana sun amince cewa ayyukan jami’an tsaron hukumar cin kwarya-kwaryar gashin kan Falasdinawa ta neman murkushe ‘yan gwagwarmaya a sansanin Jenin da ke gabar yammacin kogin Jordan ba zai hana gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila aiwatar da shirye-shiryenta a yankunan gabar yammacin kogin na Jordan ba.

Majiyoyi sun bayyana cewa: An sake samun barkewar rikici tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da jami’an tsaron hukumar cin kwarya-kwaryar gashin kan Falasdinawa a sansanin Jenin da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan.

Majiyar rundunar Jenin bangaren dakarun Sarayal-Quds da ke karkashin kungiyar Jihadul-Islamio ta bayyana cewa: Babu abin da ya rage ga hukumar Falasdinawa fiye da abubuwan da ta yi a cikin kwanaki goma da suka gabata, kuma tana son samun hanyar kwace iko da sansanin ‘yan gudun hijirar Jenin, majiyar tana mai jaddada cewa: ‘Yan gwagwarmayar Jenin sun fi karfin jami’an tsaron hukumar Falasdinawa, don haka suka kasa kai farmaki kan sansanin kai tsaye, sai dai sun tsaya a yankunan da ke kewayen sansanin, ta hanyar kai hare-hare kan fararen hula da kananan yara daga nesa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments