A sandiyyar harin da ‘yan sahayoniya su ka kawo wa Iran da asubahin yau, masana fasaahr Nukiliya da dama sun yi shahada.
Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya ambaci cewa: Daga cikin wadanda su ka yi shahadar da akwai tsohon shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta Iran; Faridun Abbasi. Shugaban jami’ar Azad, Muhammad Mahdi Dahranji. Shugaban Kwalejin fasahar Nukiliya, Abdulhamid Minochehri. Hakan nan kuma Malamin fasahar Nukiliya Ahmda Riza Zulfiqar, sai mataimakin shugaban hukumar makamashin Nukiliya Amir Husain Fiqhi.