Masana Ilimin Nukiliyar Iran Sun Yi Shahada

A sandiyyar harin da ‘yan sahayoniya su ka kawo wa Iran da asubahin yau, masana fasaahr Nukiliya da dama sun yi shahada. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya ambaci cewa: Daga cikin wadanda su ka yi shahadar da akwai tsohon shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta Iran; Faridun Abbasi. Shugaban jami’ar Azad, Muhammad Mahdi Dahranji. […]

Na’im Kassim: Harin HKI Akan Iran Ba Abinda Zai Jawo Mata Sai Kaskanci

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya yi Allawadai da harin da HKI ta kai wa Iran, wanda ya bayyana shi da cewa; Yana da hatsarin gaske, kuma ‘yan sahayoniyar sun yi hakan ne bisa cikakken goyon bayan Amurka. Sheikh Na’im Kassim ya kuma bayyana cewa; Harin na ‘yan sahayoniya ba shi […]

Birgediya Pakphur: Nan Gaba Kadan Za A Budewa “Isra’ila” Kofofin Jahannama

Sabon kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Birgadiya Muhammad Pakphur ya aike wa da jagoran juyin musulunci na Iran wasika da a ciki ya bayyana cewa: ” Laifukan ta’addanci da HKI ta aikata, wanda ya yi sanadiyyar shahadar manyan kwamandojin  da kuma  malaman Nukiliya, haka nan  mata da kananan yara da ba […]

Jagora: “Yan Sahayoniya Su Saurari Ukuba Mai Tsanani

Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya fitar da bayani a yau juma’a da a ciki ya yi wa ‘yan sahayoniya alkawalin fuskantar ukuba mai tsanani. Bayanin na jagora ya kunshi cewa: Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai Ya Ku Al’ummar Iran Masu Girma Da safiyar yau, ‘yan […]

Sojojin Iran Sun Bada Sanarwan Cewa Babu Iyaka Na Wuraren da Zasu Kai Hari A HKI

Manya-manyan jami’an sojojin kasar Iran sun bada labarin cewa a halin yanzu babu wasu kebabbun wuraren da zasu kaiwa hare-hare a HKI,. Wato hare haren zasu game ko ina a kasar. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya nakalto majiyar sojojin na fada a safiyar yau Jumma’a bayan hare haren da jiragen yakin HKI […]

Sakon Jagora : Isra’ila ta jira hukunci mai tsanani bayan hari kan Iran

Bayan harin da gwamnatin Sahayoniya ta kai kasarmu, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aike da sako ga al’ummar Iran. Ga sakon kamar haka Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai Al’ummar Iran masu daraja! Gwamnatin yahudawan sahyoniya ta hanyar aikata wani laifi da sanyin safiyar yau, ta sake bayyana […]

Rundinar IRGC, ta sanar da shahadar babban kwamandanta Manjo Janar Hossein Salami

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun sanar a cikin wani sako mai cike da alhini da shahadar Manjo Janar Hossein Salami, babban kwamandan dakarun IRGC wanda ya yi shahada da asubahin ranar Juma’ar nan yayin wani hari na ta’addanci” da gwamnatin sahyoniyawan ta kai kan hedkwatar rundunar. Hukumar soji tana jinjinawa wannan […]

Iran tana da hakkin mayar da martani ga Isra’ila : Ma’aikatar harkokin waje

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta ce mayar da martani ga gwamnatin Isra’ila hakki ne na shari’a ga Iran kamar yadda doka ta 51 ta kundin tsarin mulkin MDD ta tanada. Da farko dai ma’aikatar ta mika ta’aziyyar shahadar wasu kwamandoji da jami’an kasar Iran a harin da Isra’ila ta kai wa kasar. “Hare-haren da […]