Kasashen duniya na ci gaba da mayar da martani biyo bayan murabus din da firaministar kasar Bangaladesh Sheikh Hasina, ta yi, biyo bayan shafe makwanni na zanga zanga a kasar, wacce ta yi sanadin mutuwar daruruwan mutane.
Kungiyar Tarayyar Turai ta yi kira da a yi “tsari cikin lumana” a mika mulki zuwa ga zababbiyar gwamnatin dimokuradiyya, tare da mutunta hakkin dan Adam da ka’idojin dimokuradiyya, “in ji babban jami’in harkokin wajen EU Josep Borrell.
Jamus, ta bakin Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya ce “yana da mahimmanci a ce Bangladesh ta ci gaba da bin tafarkin dimokuradiyya”.
Amurka ta yaba wa sojojin Bangladesh tare da yin maraba da sanarwar cewa za a kafa gwamnatin wucin gadi in ji kakakin fadar White House.
A nata bangare Majalisar Dinkin Duniya, ta bakin Sakatare-Janar Antonio Guterres ta bukaci a kwantar da hankula a Bangladesh bayan murabus din firaminista Sheikh Hasina da ficewarta, ya kuma bayyana bukatar samar da “sauyi cikin lumana, cikin tsari da dimokradiyya,” in ji kakakinsa.
“Ya ci gaba da jaddada bukatar yin cikakken bincike, mai zaman kansa, ba tare da nuna son kai ba, kan tashin hankalin da akayi a kasar.” in ji mai magana da yawunsa Farhan Haq.
Ma’aikatar harkokin wajen Rasha kuwa cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce “Moscow… na fatan dawo da kasar bisa tsarin mulki cikin sauri.
A jiya ne babban hafsan sojin kasar ta Bangaladesh, ya sanar da murabus din Sheihk Hasina wacce tuni aka bayyana cewa ta bar kasar, bayan shafe shekara 15 na mulki.