Martanin kasashen Afrika game da kame shugaba Maduro na venezuela

Kasashen duniya na ci gaba da mayar da martini game da matakin AMurka na kame shugaban Venezuela Nicolas Maduro da matarsa a ranar cikin daren

Kasashen duniya na ci gaba da mayar da martini game da matakin AMurka na kame shugaban Venezuela Nicolas Maduro da matarsa a ranar cikin daren Juma’a wayewar ranar Asabar.

Su ma kasashen Afrika ba’a su a bay aba.

A sahun gaba kungiyar Tarayyar Afirka (AU), wacce ta sake nanata alkawarinta na kare dokokin kasa da kasa, girmama hurumin kasashe, da mutuncin yankunansu.

Ita ma a cikin wata sanarwa da ta fitar, Ƙungiyar Tattalin Arzikin ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) “ta ce ta amince da hakkin kasashe na yaƙi da laifukan ƙasa da ƙasa, gami da ta’addanci da fataucin miyagun ƙwayoyi,” hujjojin da Donald Trump ya gabatar don ba da hujjar kame shugaban Venezuela. Amma ECOWAS ta kuma tunatar da “al’ummar duniya wajibcinta na girmama hurimin kowace kasa,” bisa tanadin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.  

Afirka ta Kudu ita ce wata kasa daga Afrika, da ta yi martini mai karfi, inda Pretoria ta yi magana game da keta Dokar Majalisar Dinkin Duniya.

Afirka ta Kudu ta sake nanata cewa dokokin kasa da kasa ba su ba da izinin dokar matakin soja a cikin harkokin cikin gida na wata kasa mai ‘yanci ba.

Ita ma Namibiya ta yi martani mai karfi, tana bayyana “matukar mamaki” game da “keta hakkin mallaka na Venezuela da dokokin kasa da kasa.”

“Wadannan kalamai suna tunawa da zamanin mulkin mallaka inji ” Accra. “Sun kafa misali mai haɗari ga tsarin duniya. Ghana ta bukaci a saki Shugaba Maduro da matarsa.”

Haka zalika Caracas ta bayyana cewa ta yi magana da ministocin harkokin waje na kasashen Chadi, Angola, Nijar, da Gambia, kuma dukkansu sun kuduri aniyar mutunta Yarjejeniyar MDD da kuma kin amincewa da duk wani tsoma baki daga kasashen waje kan wata kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted