Martanin Kasashen Afrika Ga Shugaban Faransa

kasashen Afrika sun fara mayar wa da shugaban kasar Faransa martani game da kalaman da ya yi cewa basu da godiyar Allah, kuma ba dan

kasashen Afrika sun fara mayar wa da shugaban kasar Faransa martani game da kalaman da ya yi cewa basu da godiyar Allah, kuma ba dan kasarsa ba sun fada hannun mayaka masu ikirari da sunan jihadi.

Ministan harkokin wajen kasar Chadi, Abderaman Koulamallah ya ce “Ƙasashen Afirka, ciki har da Chadi sun taka muhimmiyar rawa wajen ceto Faransa a lokacin yake-yake na duniya, wani abu da har yanzu Faransa ba ta yi godiya akansa ba.”

Ya kara da cewa “Wajibi ne shugabannin Faransa su martaba al’ummar Afirka su kuma ga girman sadaukarwar da suka yi”.

Ya kuma ce Faransa da fake da shirye-shiryenta a Afirka wajen kare muradunta a maimakon taimakon kasashen da take hulda da su.

Shi kuwa Firaministan Senegal Ousman Sonko ya yi watsi da ikirarin da Macron ya yi kan cewa Faransa ta fice daga kasashen ne bayan tattaunawa tsakaninsu, inda ya ce Senegal ta ayyana korar Faransa ne ba tare da an gudanar da wata tattaunawa tsakanin kasashen biyu ba.

Ya kuma yi watsi da batun cewa Faransa ta taimaka wa kasashen Afirka zama masu yanci, Ya kuma zargi Faransar da ruruta wutar rikici a wasu kasashen Afirka, ciki har da Libiya.

Bayan dai da kasashen Mali, Burkina faso da Nijar suka raba gari da faransa bayan juyin mulkin sojoji, yanzu haka suna shirin ficewa daga Chadi, Senegal, da kuma Ivory Coast.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments