Manyan Malaman Roman Katolika Sun Fara Taron Zabar Paparoma

Manyan malaman addinin darikar Roman Katolika za su fara Shirin zabar shugaban darikar tasu a fadar Vatican Adadin manyan malaman addinin masu mukamin “Cardinal” 130

Manyan malaman addinin darikar Roman Katolika za su fara Shirin zabar shugaban darikar tasu a fadar Vatican

Adadin manyan malaman addinin masu mukamin “Cardinal” 130 ne za su taru a fadar Vatican, domin su zabi wanda zai maye gurbin Paparoma Farancis da ya rasu.

Sai dai masu kusancin da fadar ta Vatican suna bayyana cewa, da akwai batutuwa da dama da su ka raba kawunan manyan malaman addinin na Roman Katolika da  su ka batun auren jinsi, da rawar da mata za su taka a karkashin inuwar cocin.

Sai dai kuma wani mai sharhi akan abubuwan da su ka shafi cocin, Reese ya bayyana cewa, masu zaben za su mayar da hankali ne akan wanda zai kare ayyukan da mamacin Paparoma Francis ya bari.

Tare da cewa babu kafa ta yin yakin neman zabe a tsakanin masu mukamin na Cardinal, sai dai da akwai wasu siffofi da halaye da ake son gani da wadanda za su iya zama ‘yan takara.

Ana sanar da wanda ya zama sabon Paparoma ne ta hanyar samun kaso 2/3 na kuri’un da manyan masu zaben su ka kada.

A bisa ka’idar cocin, duk wanda aka yi wa wankan tsarki na  ” Baptisma”zai iya zama paparoma,amma  kuma tun daga 1378 ba a zabi wanda bai kai mukamin “Cardinal” ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments