Araghchi : Za’ayi Tattaunawar Iran da Amurka ta gaba a Rome bayan taron E3

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a yi taro karo na hudu na shawarwari tsakanin Tehran da Washington kan shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Rome na kasar Italiya a ranar Asabar mai zuwa. M. Araghchi ya fadawa manema labarai a gefen taron majalisar ministocin gwamnatin kasar na mako-mako yau […]

Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa Gabon

Kungiyar Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa kasar Gabon tare da maida ta a cikin cibiyoyinta. AU, ta sanar da hakan ne yayin taron kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar yau Laraba a Addis Ababa. Hakan dai ya karshen dakatarwar da aka yi wa kasar ta Gaban daga kungiyar, watanni 20 bayan […]

An kashe Falasdinawa kusan 30 a wani sabon kisan kiyashin Isra’ila a Gaza

Bayanai daga Falasdinu na cewa akalla Falasdinawa 35 dane  suka hada da kananan yara aka kashe a wanisabon kisan kiyashi na Isra’ila a zirin Gaza. A cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza, wadannan hare-haren sun yi sanadin mutuwar mutane 35 tare da jikkata 109 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata. Adadin wadanda sukayi shahada sakamakon […]

Amurka ta sake laftawa wasu kamfaninin mai na Iran takunkumi

Amurka ta sanar da kakaba takunkumi kan wasu kamfanoni 7 da ta ce suna da hannu wajen siyar da man kasar Iran, a wani mataki na kara matsin lamba duk da tattaunawar da aka yi kan shirin nukiliyar Iran. Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar ta ce, bangarorion da takunkumin ya shafa sun […]

Iran Da Iraki Sun Ce An Kammala Shimfida Layin Dogo Daga Shalamcheh Zuwa Basra

A wani taro wanda ya hada ministan riko na tattalin arziki da kudade na JMI da kuma mai bawa firai ministan kasar Iraki shawara, bangarorin biyu sun tabbatar da cewa an kammala aikin shimfida layin dogo tsakanin garin Shalamcheh na kasar Iran da kuma birnin Basra a kasar Iraki. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar […]

 Manyan Malaman Roman Katolika Sun Fara Taron Zabar Paparoma

Manyan malaman addinin darikar Roman Katolika za su fara Shirin zabar shugaban darikar tasu a fadar Vatican Adadin manyan malaman addinin masu mukamin “Cardinal” 130 ne za su taru a fadar Vatican, domin su zabi wanda zai maye gurbin Paparoma Farancis da ya rasu. Sai dai masu kusancin da fadar ta Vatican suna bayyana cewa, […]

 Bom Da Ya Tashi A Arewa Maso Gabashin Najeriya Ya Kashe Mutane 6

Wani bon kirar hannu da aka dasa akan hanyar dake hada Rann da Gamboru a jihar Borno ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 6. Daga cikin wadanda su ka rasa rayukansu sanadiyyar tashin bom din sun hada mata da kananan yara kamar yadda majiyar ‘yan sanda ta sanar. Kungiyar nan mai suna; gwamnatin musulunci a yammacin […]

 Falasdinawa 40 Sun Yi Shahada A Cikin Sa’oi 24 A Gaza

A yau Laraba sa jijjifin Safiya an sami shahidai 3 a Gaza da hakan ya kara yawan shahidai zuwa 40 a cikin sa’o’i 24. Bugu da kari, baya ga shahidan da suke faduwa a kowace rana, ana fama da matsananciyar yunwa a cikin yankin, bayan karewar kayan abincin HKI ta sake komawa yaki kwanaki 44 […]