Mali Ta Kwace Ton 3 Na Ziniya Daga Wani Kamfanin Kasar Kanada

Gwamnatin Sojan ta kasar Mali ta kwace wannan zinariyar mai yawa ce daga kamfanin hako ma’adanai na  kasar Kanada saboda rashin samun daidaito a tsakaninsu

Gwamnatin Sojan ta kasar Mali ta kwace wannan zinariyar mai yawa ce daga kamfanin hako ma’adanai na  kasar Kanada saboda rashin samun daidaito a tsakaninsu dangane da kudin harajin da ya kamata kamfanin ya bayar.

 Kamfanin dillancin labarun Associated Press ya nakalto wata wasiki da shugaban kamfani zinariya  Barric na kasar Kanada, Mark Bristow ya aike da ita zuwa ministan ma’adanai na Mali da a ciki yake  son samun takardar tabbatar da karbar zinariyar daga Bankin “Solidarity” na kasar ta Mali.

 Tun a farkon wannan watan na Janairu da ake ciki ne dai babban alkali mai bincike na kasar Mali  Boubacar Moussa Diarra, ya aike da wasika zuwa ga kamfanin na Barrick, yana mai yin gargadin cewa za a kwace zinariyar ton 3.

A jiya Litinin ne dai  wani babban jami’i a kamfanin na Barrick da ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa gwamnatin sojan ta kwace zinariyar ton 3,tare da ajiye shi a birnin Bamako.

Jami’in ya ce an dauki zinariyar ne daga wani wurin hako ma’adanai a kusa da yankin Kayes, aka kuma dauke shi  a cikin motar daukar kaya zuwa birnin Bamako.

Kudin zinariyar da aka karba, sun kai dalar Amurka miliyan 180.

Mahukuntan kasar ta Mali sun ki cewa komai akan wannan batun.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments