Ma’aikatar Harkokin Wajen Mali ta bai wa jakadan kasar Sweden umarnin barin kasarta cikin awa 72 daga ranar Juma’a, kan abin da ta kira “wasu kalamai marasa dadi” da wani ministan Sweden din ya yi.
A ranar Laraba ne Ministan Sweden na ci gaban hadin kan kasa da kasa da kasuwanci Johan Forssell, ya ce gwamnatin kasarsa ta yanke shawarar daina bai wa Mali tallafi.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Sweden ba ta ce komai ba tukunna a kan batun.