Hukumomi a Mali sun sanar da dakatar da mujallar Jeune Afrique a duk fadin ƙasar, saboda yada “zarge-zarge na karya da na tayar da zaune tsaye” a kasar.
Matakin ya shafi rarrabawa, da kuma saida mujallar a duk fadin kasar.
Hukumomin sun zargi mujallar da yada labaren karya dakan iya tada zaune tsaye da suka shafi katse samar da iskar gas, da kuma “neman afuwa ga ta’addanci.”
Matakin ya kuma ambaci “zarge-zarge marasa tushe” da “rashin daidaito a cikin rahoton,” musamman ta hanyar zarge-zargen cin zarafi da ake yi wa hukumomin kasashen kungiyar hadakar Sahel da Rundunar Sojin Burkina Faso.
Hukumomin Mali sun kara yin Allah wadai da rahoton da suka danganta da na son zuciya da son kai,” da bata suna da kuma tayar da kiyayya.”
Dama dai hukumomin Mali sun riga sun dauki irin wannan mataki game da gidajen talabijin da rediyo na Faransa da dama.
A watan Fabrairun 2024, Hukumar Sadarwa ta Mali ta dakatar da gidan talabijin na France 2 saboda keta ka’idodi na aikin jarida, da kuma farfaganda na ayyukan ta’addanci.
Haka zalika a watan Afrilun 2022, Mali ta soke lasisin aiki na Radio France Internationale (RFI) da France 24 har abada saboda yada zarge zargen karya da ke zargin sojojin Mali da kisan gilla ga fararen hula.