Malawi: Karnuna 4 sun Haddasa Rikici A Tsakanin Sabo Da Tsohon Shugaban Kasa

Rikici da jayayya sun barke a tsakanin tsohon shugaban kasar Malawi  da ya fadi a zabe, Lazarus Chakwera, da kuma sabon shugaban kasar da ya

Rikici da jayayya sun barke a tsakanin tsohon shugaban kasar Malawi  da ya fadi a zabe, Lazarus Chakwera, da kuma sabon shugaban kasar da ya ci zabe Peter Mutharika akan wanda yake da hakkin mallakar karnuka 4 masu horo na musamman dake fadar shugaban kasa.

Shi dai tsohon shugaban da bai sami nasara ba a zaben da ak ayi a watan Disambar da ya gabata, dauke karnukan 4 daga fadar shugaban kasar a lokacin da yake barinta, zuwa gidansa na kashin kasa.

A halin yanzu dai batun yana gaban ma’aikatar shari’a domin tantance wanda yake da hakkin ya mallaki karnukan 4 a tsakanin tsoho da kuma sabon shugaban kasa.

Su dai wadannan karnukan an yi musu horo na musamman ne domin iya gano makamai da ma tsatsube-tsatsube da aka iya binnewa a kasa.

Tsohon shugaban kasar ya ce, shi ne yake da hakkin mallakarsu a matsayinsa na tsohon shugaban kasa. Shi kuwa sabon shugaban kasar ya ce, karnunan mallakin gwamnati ne domin suna a matsayin ma’aikata ne, bai kamata a dauke su daga fadar shugaban kasa ba.

 Sabon shugaban kasar ya aike da ‘yan sanda 80 zuwa gidan tsohon shugaban kasar domin a dawo da karnunan, sai dai kuma Lazarus Chakwera ya ki bayar da umarnin a bude kofa.

Kasar ta fada a cikin dambaruwa saboda batun karnukan da su ka zama abin Magana a cikin majalisar dokoki da kafafen sada zumunta na al’umma da kuma kotunan kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted