Malasiya Ta Bukaci A Kori Isara’ila (HKI) Daga MDD

Ministan harkokin wajen kasar Malasiya Muhammad Hassan ya sake nanata bukatar a kori HKI daga MDD saboda kissan kare dangin da take yi a zirin

Ministan harkokin wajen kasar Malasiya Muhammad Hassan ya sake nanata bukatar a kori HKI daga MDD saboda kissan kare dangin da take yi a zirin gaza.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar ya nakalto Muhammad Hassan yana fadar haka a yau Jumma’a ya kuma kara da cewa, kasashen masu rauni a duniya sun damu da yadda manya-,manyan kasashen duniya suka kyale HKI take yin abinda taga dama a kasar Falasdinu da ta mamaye. Kuma hakan zai sa kasashe da dama su kauravewa HKI.

Labarin ya kara da cewa HKI a cikin shekaru kimani biyu da suka gabata, sun kashe falasdinawa fiye da dubu 62, amma MDD da kuma sauran kasashen yamma sun hana hatta shigar abinci a cikin zirin gaza. Alhali a gaban idommu yara kanana suna mutuwa saboda yunwa.

Ministan ya kammala da cewa, idan MDD ta kasa yin wani abut oi daddaikun kasashen duniya su dora-mata takunkuman tattalin arziki su kaurace mata, har sai hakan yayi tasiri a cikin mummunan ayyukan da take aikatawa a gaza.

Hassan yace kasar Malasiya zata gabatar da wannan batun a jawabinda zata gabatar a babban taron manya-manyan kasashen duniya a cikin watan satumba mai zuwa.

Banda kasar Malasiya wasu kasashe kamar Afirka ta kudu da kuma sauran kasashe masu tasowa sun bukaci a kauracewa HKI kan wannan kissan kiayashin da ta ke yi a gaza.

Jamia’a mai tattara rahotanni dangane da yaki a gaza, Francesca Albanese  ta bayyana kissan kare dangin da HKI take aikatawa a gaza, a matsayin irinsa mafi muni a wannan zamanin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted