Makami Mai Linzamin Iran Kirar Qasim Basir Mafarkin Ban Tsoro Ne Ga Tsarin Tsaron Makiya

Makami mai linzami kiran Qasim Basir, mafarki mai ban tsoro ga tsarin tsaron Amurka da ‘yan sahayoniyya A wata hira da aka yi da shi

Makami mai linzami kiran Qasim Basir, mafarki mai ban tsoro ga tsarin tsaron Amurka da ‘yan sahayoniyya

A wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin, ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh ya bayyana makami mai linzamin  Qasim Basir a matsayin mafi inganci na Iran.

Da yake magana game da makami mai linzami na Qasim Basir, Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh ya ce, “Sn yi amfani da wata sabuwar fasaha ta wannan makami mai linzami da ke kara karfin juriya ga hare-haren soji da na electromagnetic. Wannan makami mai linzami an kera shi ne don kada tsarin tsaron abokan gaba ya yi tasiri a kansa, kuma yana iya kai hgari daidai da inda aka harba shi. Ko da yake ba a yi amfani da wannan fasahar ba a yakin kwanaki 12 na baya-bayan nan, amma an gudanar da gwaje-gwaje masu nasara a kansa a bara.”

A ranar 5 ga watan Mayu ne, Birgediya Janar Nasirzadeh ya ba da sanarwar nasarar gwajin wannan makami mai linzami, yana mai jaddada cewa; “A gwajin mayar da martani na “Alkawarin Gaskiya ta 1da na 2″ makamin ya yi amfani da yake dauke da shi, kuma an yi nasarar gwada sabon makami mai linzami a maimakonsa.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted