Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon  Dake Takawa Makiya Birki

Kwamandan rundunar soja ta “Sayyidush-shuhada” dake Tehran Janar Qurbani Muhammad Wali Zadeh ya bayyana cewa; makamai masu linzami da Iran take da su ne, da

Kwamandan rundunar soja ta “Sayyidush-shuhada” dake Tehran Janar Qurbani Muhammad Wali Zadeh ya bayyana cewa; makamai masu linzami da Iran take da su ne, da kuma jiragen sama marasa matuki suke takawa makiya birki.”

Janar Qurbani Muhammad Wali Zadeh ya kuma ce; Albarkacin sadaukar da jinanai da shahidai su ka yi ne da kuma kwazon kwararrun masana, su ka sa Iran samun wannan karfin da take da shi.

Wali Zadeh wanda ya halarci taron girmama rundunar sa-kai ta Basiji da kudancin birnin Tehran, ya kara da cewa, Iran ta samu matsayin da take da shi ne a wannan lokacin daga jihadin shahidai da tsayin dakar al’ummar Iran, sannan kuma ya kara da cewa; A halin yanzu karfin Iran a fagen makamai masu linzami ya kai kolin da makiya suka kwana da sanin cewa duk wata barazana ta kawo wa jamhuriyar musulunci hari, zai fuskanci martani mai tsanani.

Haka nan kuma ya ce; Al’ummar Iran ba ta taba zama mai tsokana da fara kai hari ba a cikin kowane fada, amma kuma ba ta ja da baya a gaban barazanar makiya.

Janar din sojan na Iran ya yi Ishara da martanin da Iran din ta mayar bayan shahadar Janar Shahid Kassim Sulaimani da ya tabbatar da karfinta na  kare kai. Wannan karfin ne yake hana abokan gaba tarbar aradu da ka, su kawo wa Iran din hari.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted