Majiyar Gwamnatin Yamen Ta Ce HKI Ta Kai Wasu Sabbin Hare-Hare Kan Kasar

Jiragen yakin HKI sun kai sabbin hare-hare kan kasar Yemen a yau Laraba, inji tashar talabijin ta Al-Masirah na gwamnatin kasar. Labarin ya kara da

Jiragen yakin HKI sun kai sabbin hare-hare kan kasar Yemen a yau Laraba, inji tashar talabijin ta Al-Masirah na gwamnatin kasar.

Labarin ya kara da cewa yahudawan sun kai hare-haren ne a tsakanin wasu duwatsu a cikin kasar, da kuma kan cibiyar kungiyar Ansarullah da ke tsakiyar birnin San’a babban birnin kasar, da kuma ma’aikatar tsaron kasar.

Wadanda suka ganewa idanunsu sun bayyanawa kamfanin dillancin labaran reuters kan cewa yahudawan sun kai hare-haren kan wani barikin soja ne a yau Laraba.

Kafin haka dai sojojin Yemen sun kai kaiwa HKI hare-hare a gewayen birnin Qudus da kuma tashar jiragen saman da Ramona da ke kudancin kasar kusa da birnin Ummu Rashrash ko Ilaat kamar yadda yahudawan suke kiransa.

Gwamnatin kasar Yemen dai ta shiga yaki da HKI ne tun watan Octoban shekara ta 2023 tare da manufar tallafawa Falasdinawa a Gaza wadanda HKI takewa kissan kiyashin kusan shekaru biyu Kenan.

Share

4 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted