Sheikh Qasim: Hare-Haren HKI Kan Qatar Sashe Ne NA Shirinta Na “Isra’ila Babba”

Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Naem Qaseem yace hare-haren da HKI ta kai kan kasar Qatar yana daga cikin shirinta na samar da ‘Isra’ila Babba’ Kuma gwamnatin kasar Amurka tana goyon bayan hakan. Sheikh Naeem Qasem ya bayyana haka ne a yau Laraba a lokacinda yake jawabi ta kafar Bidiyo, dangane da […]

Majiyar Gwamnatin Yamen Ta Ce HKI Ta Kai Wasu Sabbin Hare-Hare Kan Kasar

Jiragen yakin HKI sun kai sabbin hare-hare kan kasar Yemen a yau Laraba, inji tashar talabijin ta Al-Masirah na gwamnatin kasar. Labarin ya kara da cewa yahudawan sun kai hare-haren ne a tsakanin wasu duwatsu a cikin kasar, da kuma kan cibiyar kungiyar Ansarullah da ke tsakiyar birnin San’a babban birnin kasar, da kuma ma’aikatar […]

Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan Al-Mujtaba (a) 138

138- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane, Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana […]

Araqchi Ya Isa Kasar Tunisiya A Wata Ziyarar Aiki Da Ya Kai.

Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya isa kasar tunisiya domin tattaunawa da hukumomin kasar, a ci gaba da ziyarar da yake yi a yammacin Afrika, bayan da ya bar kasar masar inda ya gana da directan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya  kuma suka cimma matsaya tsakaninsu, An […]

Babu  Gaggawa Na Fara cire  Haraji Kashi 5 Na Man Fetur A Nijeriya

famfon mai

Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun ya bayyana cewa ba za a fara aiwatar da shirin cire harajin man fetur na kashi 5 cikin 100 ba nan take. Ministan ya fadi  hakan ne a ranar Talata a wani taron manema labarai a ofishinsa da ke Abuja. Ministan ya kuma ce ba za a […]

Da Alama Nijeriya Ta Rasa Tikitin Kai Tsaye Na Zuwa Gasar Kofin Duniya 

Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta buga kunnen doki da takwararta ta Afirika Ta Kudu da ci 1-1 a filin wasa na Toyota dake birnin Bloemfontein dake kasar Afirika Ta Kudu. Kyaftin din Nijeriya Troost Ekong  shi ne ya ci gida a minti na 25 da fara wasan kafin nan dan wasan bayan Nijeriya Calvin […]

Iran Da Hukumar IAEA Sun Fahimci Juna Kan Shirinta Na Nukiliya .

Kakakin Maikatar harkokin wajen kasar iran ismail baqa’I ya sanar cewa an fahimci juna tsakanin Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya duniya game da shirin ta na nukiliya na zaman lafiya,  wanda hakan ke nuna cewa a kowanne lokacin iran tana shirinta ne domin ayyukan zaman lafiya tare da tuntubar IAEA sabanin parpagandar da  […]

Harin Isra’ila A Qatar ya kalubalanci Grantin Tsaron Amurka

A jiya ne HKI ta kai hari a kasar Qatar daya daga cikin kawayen Amurka da ta girke sansanin sojin Amurka mai girma a yammacin Asiya, wanda ke kara tabbatar da cewa lallai alkawarin Amurka na bada tsaro ga kasashen kawayenta bashi da wata kima Harin na isra’ila a Qatar ya afku ne duk da […]

Me yasa za mu je Gaza a cikin jiragen ruwa na tawagar “Sumoud” na duniya?

“Jared Sacks” da “Zukiswa Wanner,” marubuta da masu fafutukar al’adu da ke zaune a Cape Town, sun rubuta a cikin wata kasida ga Al Jazeera mai taken “Me yasa za mu je Gaza tare da jiragen ruwa na ‘Sumoud’ na duniya?”: Mun tashi don ci gaba da bege. Rasa bege na nufin watsi da mutanen […]