Yan majalisar dokokin kasar Jamus sun bukaci shugaba Friedrich Merz ya saye man diesel daga kasar Rasha kamar yanda Amurka ta yi.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto yan majalisar suna fadar haka a wani zaman a musamman don tattaunwa wannan batun a birnin Berlin.
Labarin ya kara da cewa a ranar Jumma’an da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwan cewa ya sasanta da Putin kan sayen man diesel don amfanin Amurkawa, wadanda suke cikin halin kakanikaye saboda rufe mashigar ruwa ta Hurmuz.
Farashin makamashi ya karu fiye da yanda ake tsammi tun bayan da JMI ta sami nasarar rufe mashigar ruwa ta Hurmuz watanni 7 da suka gabata.
Kasar Jamus kamar sauran kasashen Turai da Amurka, suna fama da karancin man diesel da kuma tsadar farashinsa. Don haka inji ya majalisar kasar ta Jamus ita ma kamar yanda Amurka ta yi ta shiga tattaunwa da Putin don sayen man diesel da farashi mai sauki wanda zai sawwake rayuwar mutanen kasar sannan yatallafawa manya manyan kamfanonin da suke fama da karacinsa.
Jam’iyyun adawa na kasar wadanda kuma suke da rinjaye a majalisar dokokin kasar sun bukaci shugaba Merz yayi hakan.
Shugaban Amurka Donal Trump dai yana son ya sauke farashin makamshi kafin zaben watan Nuwamba mai zuwa, don ya samu jam’iyyarsa ta sami rinjaye a majalisun dokokin kasar na sanatoci da wakilai.