Bayan sanarwar da E3 (Faransa, Jamus, da Burtaniya) suka yi na haifar da hanyar da za ta kai ga dawo da takunkumin da aka kakaba wa Tehran kan shirinta ma nukiliya, Majalisar Dokokin Iran ta tsara tare da gabatar da wani kudirin doka na gaggawa da ke ba da shawarar ficewa gaba daya daga yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT).
Hossein-Ali Haji-Deligani, Mataimakin Shugaban Kwamitin Mataki na 90 na Majalisar Dokokin Iran, ya tabbatar da cewa za a shigar da kudirin zuwa tsarin majalisar a rana mai zuwa sannan a sake duba shi a wani budadden zama.
“Kamar yadda muka fada a baya, wadannan kasashe sun riga sun fara aiwatar da takunkumin da aka kakaba mana. Babu wani sabon abu a cikin wannan.” Haji-Deligani ya shaidawa Tasnim na Iran.
Ya kara da cewa matakan da aka dauka su ne “mafi karancin martani da majalisar ta bayar kan matakin da kasashen Turai suka dauka na baya-bayan nan.”
Wannan doka da aka gabatar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna bacin rai a Tehran dangane da gazawar kasashen yammacin duniya wajen mutunta yarjejeniyoyi da kuma sassauta matsin lamba kan Iran.