Kakakin Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Takunkumin da Amurka ta kakaba wa Iran zai cutar da talakawa ne kawai
Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stéphane Dujarric, wanda ke mayar da martani ga yakin tattalin arziki da takunkumin da Amurka ta kakaba wa Iran, ya bayyana cewa: Takunkumin yana cutar da talakawa ne kawai.
A tambayar da wakilin kamfanin dillancin labaran IRNA ya yi ga kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric cewa: Wani mataki babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya zai dauka wajen kalubalantar takunkumin da Amurka ta kakaba wa Iran, wanda zai kawo cikas ga damar mutane na samun magunguna da kuma tsaron tafiye-tafiyen jiragen sama, keta Dokar Majalisar Dinkin Duniya da kuma laifi ga bil’adama, kuma wane mataki zai dauka?
Kakakin Majalisar Dinkin Duniya ya amsa da cewa: “Duba da cewa: Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya yana nuna damuwarsa akai-akai game da karuwar amfani da takunkumin bangare guda, kuma duk yadda aka je aka dawo takunkumin da ake kakabawa a karshe yana cutar da talakawa.”
Amurka, wacce ta sanya takunkumi kan Iran tsawon shekaru da dama, tana ci gaba da aiwatar da burinta na tilasta wa Iran din mika wuya ta hanyar yakin tattalin arziki da fadada iyakokin takunkumin, bayan shan kaye a yakin soja na hadin gwiwa da kungiyar ‘Yan Sahayoniyya kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma sojojin Iran da al’ummar kasar.