Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Fatali Da Batun Kafa Gwamnatin Hadaka A Kasar Sudan

Gwamanatin Sudan ta yi maraba da sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na yin Allah wadai da shirin kafa gwamnatin hadaka a kasar Sudan

Gwamanatin Sudan ta yi maraba da sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na yin Allah wadai da shirin kafa gwamnatin hadaka a kasar Sudan

Sudan ta yi marhabin da sanarwar da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar a jiya Laraba, inda ta yi watsi da shirin dakarun kai daukin gaggawa na kafa gwamnatin hadaka a yankunan da ke karkashinta. Sanarwar ta yi gargadin cewa wannan matakin na barazana ga hadin kan kasar, kuma yana iya yin kasadar kara ta’azzara rikicin, yayin da aka dakile wani hari da dakarun kai daukin gaggawa na kungiyar Rapid Support Forces suka kaddamar a yankin kudu da kudu maso yammacin birnin El Fasher.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta fitar, ta bayyana kudurin gwamnatin kasar na tabbatar da tsaron kasar, tsaro, zaman lafiyar kasar, hadin kai, da ‘yancin kan yankunanta.

Ta kuma tabbatar da shirinta na yin aiki tare da kasashen duniya bisa ka’idoji da dokokin da suka dace da muradun al’ummar Sudan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted