Majalisar Dinkin Duniya Ta Karyata Zargin Gwamnatin Mamayar Isra’ila

Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Matakin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta dauka na rushe-rushen cibiyoyin kiwon lafiya a Gaza “laifi ne na yaki”

Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Matakin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta dauka na rushe-rushen cibiyoyin kiwon lafiya a Gaza “laifi ne na yaki”

Hukumar kare hakkin bil-Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin mamayar Isra’ila ke kai wa kan asibitoci a Zirin Gaza sun zame manyan laifukan yaki, don haka tana mai matukar nuna damuwa kan wannan rashin mutunta dokokin kasa da kasa da na kare hakkin bil’adama.

Hukumar ta kara da cewa a cikin wata sanarwa da ta fitar, wannan ta’asar ta janyo rugujewar tsarin kula da kiwon lafiya a Zirin Gaza gaba daya, inda ta yi nuni da cewa, ta tattara rahotonni akalla farmaki kan asibitoci 27 har sau 136 da wasu cibiyoyin kiwon lafiya 12.

Hukumar ta kara da cewa: Zargin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi cewa ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa suna amfani da asibitoci a matsayin wuraren kai hare-hare da cewa: Ba gaskiya ba ne kuma babu wani dalili komai kashinsa da ke tabbatar da ikirarinta.

Sanarwar ta Hukumar Lafiya ta ce: Hare-haren da gwamnatin mamayar  Isra’ila ta kai ya haifar da mummunar barna a asibitin Kamal Adwan, kuma an gano manyan kaburbura guda 3 tare da gano gawarwaki sama da 80.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments