Majalisar Dinkin Duniya Ta Ce: Sudan Ta Shiga Rikicin Jin Kai Da Ba A Taba Ganin Irin Ta Ba

Mjalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi game da rikicin jin kai a Sudan wanda ba a taba ganijn irinsa ba Clement Salami, jami’ar kula da

Mjalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi game da rikicin jin kai a Sudan wanda ba a taba ganijn irinsa ba

Clement Salami, jami’ar kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan, ta yi gargadin cewa matsalar jin kai a wannan kasa ta kai wani abin da ba a taba gani ba.

Ta ce – a cikin wata sanarwa da ta fitar – fiye da rabin al’ummar Sudan na bukatar agajin gaggawa da kariya, ciki har da yara miliyan 16, kamar yadda ta bayyana.

Salami ta bayyana cewa, matsalar karancin abinci da ake fama da ita a kasar Sudan ta kai matsayin tarihi, musamman a yankunan yankin Darfur, babban birnin kasar, Khartoum, da kuma yankin Kordofan.

Ta kuma ce bayan shafe sama da watanni 20 ana yaki tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces, Sudan tana fuskantar matsalar jin kai mafi girma a duniya.

Jami’ar ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga dukkan bangarorin da ke rikici a Sudan da su saukaka isar kayayyakin jin kai, da kuma tabbatar da tsaron ayyukan jin kai da ma’aikatan agaji a kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments