Majalisar dinkin duniya ta ce, akalla yara 15 ne suka mutu sakamakon wani harin jirgi maras matuki da aka kai kan wani sansanin ‘yan gudun hijira a Sudan. kuma Harin ya afku ne a garin Al Sunut da ke jihar Kordofan ta Yamma.
Rahotannin farko daga ofishin kare hakkin dan Adam na Majalisar Ɗinkin Duniya sun nuna cewa ana zargin sojojin Sudan da kaddamar da harin.
Baya ga yara 15 da suka mutu, akalla fararen hula 26 ne aka kashe a wannan harin na Al Sunut, yayin da wasu da dama suka jikkata.
Asusu tallafawa kananan yara ta Majalisar dinkin duniya (UNICEF) ya yi Allah-wadai da wannan hari, tare da cewa rayuwar yara a Sudan na ci gaba da fuskantar barazana mai tsanani a sansanonin da suka fake don tsira daga yunwa da kuma yaki.