Majalisar datawa ta Aljeriya, ta amince da tura rundunar sojoji zuwa Nijar, a wani mataki da ba a taɓa ganin irinsa ba tun bayan yakin Oktoban 1973 tsakanin Masar da Siriya da kuma Isra’ila a dayan gefen.
Kuri’ar majalisar ta gudana ne a lokacin zaman sirri, inda aka gayyaci membobin Majalisar a ranar Alhamis a karƙashin sunan “taron gaggawa.”
Matakin ya samu karbuwa a mataki mai karfi don goyon bayan shawarar shugaban kasar na ba da izinin tura rundunar sojoji zuwa Nijar.
Membobin Majalisar sun shaida wa manema labarai cewa wannan ya kunshi “tura rundunar sojojin ƙasa don tabbatar da tsaron ayyukan mai mallakar kamfanin Sonatrach na Aljeriya a wannan ƙasa maƙwabciya.”
Wannan matakin dai na zuwa ne bayan da a ranar Larabar da ta gabata, kasashen Aljeriya da Nijar suka sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna kan haɗin gwiwar soja, a cewar wata sanarwa daga Ma’aikatar Tsaro ta Aljeriya.
An sanya hannu kan yarjejeniyar ne bayan ganawa tsakanin karamin Ministan Tsaro, kana Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Aljeriya, Laftanar Janar Saïd Chengriha, da Ministan Tsaro na Nijar, babban Janar Salifou Mody, wanda ya ziyarci ƙasar ta Aljeriya.
Tsawon watanni da dama, Aljeriya da Nijar sun ƙarfafa haɗin gwiwarsu sosai a fannoni da dama, ciki har da haɗin gwiwar siyasa, diflomasiyya, soja, da tattalin arziki, bayan wani lokaci na tsamin dangantakarsu.