Mahukuntan Sudan Sun Ce Babu Batun Sulhuntawa Da ‘Yan Tawayen Kasar

Mataimakin shugaban majalisar gudanar da Mulki a Sudan ya jaddada cewa: Ba zasu amince da duk wani shirin wanzar da zaman lafiya da sulhu da

Mataimakin shugaban majalisar gudanar da Mulki a Sudan ya jaddada cewa: Ba zasu amince da duk wani shirin wanzar da zaman lafiya da sulhu da ‘yan tawayen kasar ba

Mataimakin shugaban majalisar gudanar da Mulki a Sudan Malik Agar, ya ce: Nan kusa kadan, za a kawo karshen yakin Sudan tare da murkushe ‘yan tawaye da suka nemi wargaza kasar, don cimma munanan bukatunsu. Yana mai jaddada cewa ba zasu amince da duk wani shirin samar da zaman lafiya da sulhu da zai shafi ‘yancin kasar ba.

A cikin wani jawabi da Aqar ya gabatari, kwana guda bayan da sojojin Sudan suka kwace ikon da birnin Wad Madani, fadar mulkin jihar Al-jazira daga hannun dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces, ya ce: Nasara tana kusa, yana mai jaddada cewa: Mika mulki ga tsarin dimokradiyya na bukatar kammala kwato dukkan sassan kasar nan daga ‘yan tawayen kungiyar Rapid Support Forces.

Aqar ya jaddada cewa: “Ba za su amince da duk wani shirin samar da zaman lafiya da zai maido da ‘yan tawayen kasar fagen siyasa ba,” ya kara da cewa: “Ba za su amince da duk wani shirin zaman lafiya da ya shafi ‘yancin Sudan ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments