Shugaban kasar Venezuela Nicholas Maduro ya fada a yau Asabar cewa, kasarsa tana ci gaba da aiwatar da shirinta na jan damara da yin turjiya da kare kasa a wani Shirin na musamman da zai ci gaba har zuwa 2031. Haka nan kuma ya ce:
“Pargandar bata suna da Amurka take yi manufarta shi ne satar albarkatun da Alalh ya huwacewa wannan kasar domin biyan bukatun tattalin arziki na tsarin jari-hujja.
A cikin watannin bayan nan dai Amurka ta tsananta takurawar da take yi wa kasar Venezuela ta hanyar kai wa jiragen ruwan da suke fitowa daga cikinta hare-hare da kuma kwacen masu dauke da man fetur.
Shugaban kasar ta Venezuela ya kira yi shugaban kasar Amurka da ya mayar da hankali wajen warware matsalolin cikin gidanta.
Amurka dai ta girke jiragen ruwa na yaki masu yawa a cikin tekun Carrebia, da ya zuwa yanzu ta kashe mutane 100 ta hanyar hare-haren da take kai wa kananan jiragen ruwan da ta ce, suna dakon muggan kwayoyi.
Shugabannin kasashen yankin da su ka hada da Brazil suna ci gaba da yin tir da halayyar ta Amurka wacce take kokarin dawo da yakar kasashen yankin da ta yi a shekarun baya.