A Madagaska gobe Juma’a ne kotun tsarin mulkin kasar zata rantsar da Kanar Michael Randrianirina a matsayin shugaban kasa.
Hakan na zuwa ne bayan majalisar dokokin kasar ta tsige shugaban kasar Andry Rajoelina bayan ya tsere daga kasar sanadiyyar zanga zangar data rikide zuwa bore wa gwamnatinsa saboda matsalar wutar lantarki da ruwan sha.
Tunda farko dai kanar Randrianirina ya kiyasta zai rike mulki na wa’adin watanni 18 zuwa 24 lokacin da za’a kai ga gudanar da zaben raba gardama na kundin tsarin mulkin kasar.
Saidai kotun tsarin mulkin kasar ta sanar da cewa, ya kamata a gudanar da zaben sabon shugaban kasa cikin kwanaki 60.
Tuni Tarayyar Afirka (AU) ta dakatar da kasar ta Madagascar daga kungiyar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar Talata.