Madagaska : Ranar Juma’a za’a rantsar da Kanar Randrianirina

A Madagaska gobe Juma’a ne kotun tsarin mulkin kasar zata rantsar da Kanar Michael Randrianirina a matsayin shugaban kasa. Hakan na zuwa ne bayan majalisar dokokin kasar ta tsige shugaban kasar Andry Rajoelina bayan ya tsere daga kasar sanadiyyar zanga zangar data rikide zuwa bore wa gwamnatinsa saboda matsalar wutar lantarki da ruwan sha. Tunda […]
Pezeshkian Ya Yi Gargadi Akan Makircin Makiya A Tsakanin Al’ummar Musulmi

Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa a koda yaushe makiya suna neman haifar da rikici tsakanin kasashen musulmi domin raunana su, yana mai nuni da barkewar tashin hankali tsakanin Pakistan da Afghanistan. Mr. Pezeshkian ya bayyana haka ne a yayin wani taro inda ya fayyace matsayin kasar Iran dangane da takun saka […]
Euro-Med ta bukaci bangarori su shiga Gaza domin tattara bayanai kan kisan kiyashin Isra’ila

Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta Euro-med mai hedkwata a Geneva ta yi kira ga kasashen duniya da su tabbatar da shiga Gaza ba tare da ‘yan jarida, masu bincike, da masana harkokin shari’a don tattara bayanan kisan kiyashin da Isra’ila a Gaza da kuma hukunta wadanda suka aikata laifin. A cikin wata sanarwa da […]
Kenya : An dawo da gawar Raila Odinga gida

A Kenya dubban al’ummar kasar ne suka hallara a babban filin jirgin saman kasar domin tarben gawar tsohon Firaministan kasar Raila Odinga. Shugaban kasar, William Ruto da tsohon shugaban kasa Uhuru Kenyatta da manyan jami’an gwamnati na daga cikin wadanda suka tarbi gawar tare da iyalan Odinga. Raila Odinga ya mutu ne a ranar Laraba […]
Iran Ta Bukaci Kasashen Kungiyar NAM Su Hada Kai Don Fuskantar Rashin Bin Doka Da Oda A Duniya

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a jawabin da ya gabatar a taron tsakiyar shekara ta ministocin harkokin wajen kungiyar yan ba ruwammu wato NAM a birnin Kampala babban birnin kasar Uganda a jiya Laraba, ya jadda bukatar hadin kai da goyon baya a tsakanin kasashen kungiyar, wajen fuskantar rashin mutunta dokokin kasa da […]
Iran: Yawan Karafan Da Ake Sayarwa Zuwa Kasashen Waje Ya Kai Dalar Amurka Billion $4

Ma’aikatar masana’antu da ma’adinai ta kasar Iran ta bayyana cewa na sami karin ci gaba a yawan karfen da kasar ke sayarwa ga kasashen waje a rabin farko na wannan shekara ta 2025 zuwa dalar Amurka billion $4. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa duk tare da takunkuman tattalin arzikin da […]
Falasdinu: Masu Gadin Gidajen Yari A HKI Sun Sun Daki Marwan Barghouti Har Ya Suma

Majiyar hukumar fursinoni ta Falasdinawa ta bada sanarwan cewa masu gida a gidajen yarin HKI sun daki Marwan Barghouti a cikin makon da ya gabata har ya suma, kuma sun karya masa awaza har guda 4 sanadiyyar haka. Jaridar ‘The National’ ta kasar Amurka bayyana cewa Barghouti yana daga cikin shuwagabannin Falasdinawan da Hamas ta […]
Venezuela Ta Bada Sanarwan Sabbin Matakan Tsaro A Kan Iyakar Kasar Da Colombia

Shugaban kasar Venezuelan Nicolás Maduro ya bayyana sabbin matakan tsaro a kan iyakar kasar da kasar Colombia bayan da gwamnatin Amurka ta sabonta sabbin matakai na nuna adawa da gwamnatin kasar. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa shugaban ya shelanta wannan sabbin matakan tsaro ne bayan da gwamnatin shugaba Trump ba […]
Tarayyar Afirka AU, Ta Jingine Samuwar Madagaska Daga Cikin Kungiyar

Bayan juyin mulkin da aka yiwa Andry Rajolina a kasar Madagaska kungiyar tarayyar Afirka ta bada sanarwan jingine kasar daga zama mama a cikinta har zuwa abinda hali yayi. \ Tashar talabijin ta Almayadin ta nakalto majiyar kungiyar AU na bada wannan sanarwan, kwana guda bayan da sojoji suka yi juyin mulki wa shugaba Andria […]
Iran Ta Jaddada Cewa: A Shirye Take Ta Tattauna Amma Ba Zata Amince Da Juya Akalarta Ba

Shugaban Majalisar Dabarun Kula da harkokin waje kuma mamba a Majalisar fayyace manufofin kasar Iran ya bayyana cewa: Iran a shirye take ta tattauna amma ta kin juya akalarta Shugaban majalisar dabarun kula da harkokin waje kuma mamba a majalisar fayyace manufofin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Kamal Kharrazi, ya jaddada cewa: Iran a shirye take […]
Kasashen Iran Da Tunusiya Sun Jaddada Karfafa Alaka A Tsakaninsu A Bangarori Da Dama

Ministan harkokin wajen kasar Iran da takwaransa na Tunisiya sun jaddada cewa: Warware matsalar Falasdinu na bukatar kawo karshen mamayar da ake yi Ministocin harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Tunisiya sun jaddada cewa: Warware matsalar Falastinu na bukatar kawo karshen mamaya da kuma tabbatar da hakkin al’ummar Falastinu na cin gashin kansu. Wannan […]
Kasar Afirka Ta Kudu Ta Jaddada Aniyarta Ta Ci Gaba Da Shari’ar Neman Hukunta Isra’ila Kan Batun Gaza

Kasar Afirka ta Kudu tana ci gaba da shari’ar da ta shigar kan gwamnatin mamayar Isra’ila duk da tsagaita bude wuta da aka yi a Gaza Ma’aikatar huldar kasa da kasa da hadin gwiwa ta Afirka ta Kudu ta tabbatar da cewa: Tsagaita bude wuta a zirin Gaza ba zai kawar da laifukan da aka […]
Gwamnatin Kamaru Ta Gargadi Dan Takarar Da Ya Shelanta Kansa A Matsayin Wanda Ya Lashe Zabe

Ministan Harkokin Cikin Gida Ya Yi Watsi Da Shelanta Samun Nasara Da Dantakara Isa Bakari Ya Yi Ministan harkokin cikin gidan kasar Kamaru Paul Atanga Nji ya yi watsi da yadda dan takarar shugabancin kasar Isa Tchiroma Bakari ya shelanta kansa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa, ya kuma yi kira ga shugaban […]
Ministocin Harkokin Wajen Kungiyar NAM Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Venezuela

Ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar ‘yan baruwanmu a taronsu karo na 19 da ke gudana a birnin Kampala na kasar Uganda a ranakun 15 da 16 ga wannan wata na Oktoban 2025, sun bayyana matukar damuwarsu kan halin da ake ciki a yankin Caribbean, tare da tabbatar da cikakken goyon bayansu ga Jamhuriyar Venezuela wajen […]