Macron Da Yariman Saudiyya Sun Tattauna Kan Lebanon Da Gaza

Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman (MBS) da shugaban Faransa sun tattauna “kokarin diplomasiyya na tabbatar da tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila

Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman (MBS) da shugaban Faransa sun tattauna “kokarin diplomasiyya na tabbatar da tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Lebanon”, a cewar wata sanarwa daga ofishin Macron.

“Babban burin shugaban kasar da kuma Yarima mai jiran gado shi ne samar da tsagaita wuta ba tare da bata lokaci ba a Gaza, domin kubutar da dukkan wadanda aka yi garkuwa da su, da kare fararen hula ta hanyar isar da kayayyakin jin kai da kuma ba da gudummuwa wajen nemo mafita ta siyasa,” in ji sanarwar.

Bangarorin sun kuma yi kira da a gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Lebanon domin hada kan ‘yan kasar tare da aiwatar da sauye-sauyen da suka wajaba don tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasar.

Majalisar dokokin kasar Lebanon za ta yi taro domin zaben sabon shugaban kasa a ranar 9 ga watan Janairu, 2025, kamar yadda kakakin majalisar Nabih Berri ya sanar a makon da ya gabata, sama da watanni 12 bayan yunkurin karshe na zaben shugaban kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments