Mataimakin kwamandan dakarun kare juyin musulunci na kasar iran ya jaddada cewa sojoji da dakarun kare juyin musulunci na iran sun shirya tsaf don kare mashigar Hurmuz daga duk wata barazana, kuma mashigar tana karkashin kulawar dakarun kasar iran ne, wanda kullum suke kara daukar matakai a wajen.
Major janara Mustafa Izadi yayi wannan bayanin ne a daren jiya alhamis a wata ziyara da ya kai a sansanin dakarun IRGC na madinatul munawara domin duba irin shirin da aka yi na kare kasar ta kasa a mashigar Hurmuz da tsibiran kasar iran dake tekun farisa daga duk wani shishshigi.
Haka zalika ya kara da cewa yanayin da ake ciki a kasa yana nuna shirye-shiryen yaki na dakarun tsaro da kuma kudurin mayakan wadanda jama’a da dakarun Basij ke kan gaba a cikinsu, wadanda suka halarci wurin sadaukarwa domin kare mauradun juyin musulmi da kuma aiwatar da umarnin babban kwamadan dakarun soji na kasar wato ayatollah sayyid mujtaba khamane’i