Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta rage tuhumar da ake yi wa Shugaban Venezuela Nicolás Maduro, inda ta janye manyan tuhume-tuhumen da Donald Trump ya gabatar na cewa Maduro ne ke jagorantar wata kungiyar masu safarar miyagun kwayoyi.
Tuhume-tuhumen farko, wanda ke kunshe a cikin tuhumar 2020, ya bayyana ”Cartel de los Soles ”a matsayin wata kungiya mai tsattsauran ra’ayi da ake zargin Maduro ne ke jagoranta, wadda ake zargi da hannu a safarar hodar iblis mai yawa.
Wannan tuhume-tuhumen, wanda Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta janye yanzu, ya zama tushen matsin lamba na Washington kan gwamnatin Caracas.
A watan Yulin 2025, Ma’aikatar Baitulmalin Amurka ta ayyana kungiyar a matsayin kungiyar ta’addanci, wani hukunci da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio da tsohon Mai Ba da Shawara kan Tsaron Kasa Robert C. O’Brien suka goyi baya.
An kame Nicolas Maduro da matarsa ne a ranar Asabar daga gidansu da ke Caracas, sannan aka nufi New York dasu domin a yi musu shari’a a Amurka.