Ma’aikatar  Harkokin Wajen Iran Ta Mayar Da Martani Kan Kudurin Tawagar Turai

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta mayar da martani ga Tawagar Turai na kokarin dawo da takunkumi kan kasarta Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar da

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta mayar da martani ga Tawagar Turai na kokarin dawo da takunkumi kan kasarta

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar da sanarwa a matsayin martani ga sanarwar da Tawagar Tura ta yi wa kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da baya kan ka’ida dangane da kuduri mai lamba 2231.

Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da kakkausan harshe tare da yin Allah wadai da shelanta batu da baya kan doka da tawagar Turai Faransa da Jamus da Birtaniya suka yi ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya dangane da kuduri mai lamba 2231 na shekara ta 2015. Wannan matakin bai dace ba, wanda ya ci karo da Tsarin Raba Rikici (DRM) na Haɗin gwiwar Shirye-shiryen Aiki (JCPOA), kuma yunƙuri ne da baya bisa doka ko ƙa’ida, na dawo da kuduri da ya sude, kuma hakan a fili ya saba wa ƙuduri na mai                      lamba 2231 na shekara ta 2015.

Kamar yadda wasu mambobin majalisar musamman kasashen China da Rasha suka jaddada cewa; Kasashen Turai uku ba su bi ka’idoji da matakai da aka tanada a cikin yarjejeniyar nukiliya da kuma kuduri mai lamba 2231 ba. Don haka sanarwar tasu wani yunkuri ne mai cike da kura-kurai da saba doka da aka tanada na amfani da kuduri mai lamba 2231 don aiwatar da manufar siyasa ta nuna son kai kan Iran.

Yemen

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments