Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran ya bayyana cewa: Tsaftatacciyar rayuwa ita ce koyarwar tabbatar da rayuwa mai nagarta
Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Hujjatul-Islam Ali Akbari ya bayyana cewa: Ana gudanar da cikakken yaki a kan tsarin iyali, inda ake amfani da yada rashin kamun kai da lalacewar tarbiyya a matsayin makami; yayin da rayuwa mai tsafta da kamewa ita ce tushen samun “rayuwa mai inganci da take kai ga tushen sanun rayuwa ta gari mai cike da alheri a fagen rayuwa”.
A cewar kamfanin dillancin labaran Mehr, Hujjatul-Islam Hajj Ali Akbari da ya jagoranci sallar Juma’a a yau a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran ya jaddada rawar da kamun kai ke takawa wajen inganta dangantakar zamantakewar jama’a, yana mai cewa: “Daga mahangar koyarwar addinin Allah, hankali da gogewar tarihi ta mutane, za a ga kamun kai yana matsayin ka’ida ce ta zinare kuma ginshiƙi mai mahimmanci wajen tabbatar da farin ciki da walwala da ci gaban al’umma baki daya.”
Yana mai kira ga masu ibada da su yi riko da tsoron Allah tare da komawa kan tattaunawar da aka yi a baya game da rayuwa mai tsarki da kamewa, yana mai fayyace cewa: “Kamewa tana ɗaya daga cikin fitattun alamomin tsoron Allah, kuma ginshiki ne na asali wajen daukaka ɗabi’ar ɗan adamtaka a kan hanyar ci gaban imani.”