Limamin Tehran:  Tarayyar Turai Ba Ta Da ‘Yanci Na Kashin Kanta

Wanda ya jagoranci sallar juma’a a nan birnin Tehran a yau Hujjatul-Islam Wal Muslimin Hassan Abu Turabi, ya bayyana cewa;  ko kadan tarayyar turai ba

Wanda ya jagoranci sallar juma’a a nan birnin Tehran a yau Hujjatul-Islam Wal Muslimin Hassan Abu Turabi, ya bayyana cewa;  ko kadan tarayyar turai ba kungiya ce wacce take da ‘yancin kanta ba.

Limamin na birnin Tehran wanda ya yi ishara da bayanin hadin gwiwa da kasahen turai su ka fitar akan Iran wanda ya kunshi tuhume-tuhume mara tushe  akan shirinta na Nukiliya na zaman lafiya, ya ce ba su ginu akan hankali ba.

Da  yake magana akan alakar Iran da kasashen turai, limamin na Tehran ya ce; Tun bayan cin nasarar juyin musulunci alakar bangarorin biyu ta ga fadi tashi,amma yanzu an wayi gari kasashen na turai ba su da ‘yanci na kashin kansu.

Hari ila yau, limamin na Tehran  da yake magana akan bude tattaunawa a tsakanin Iran da kasashen turai, ya ce,babu yadda za a yi Iran ta yi tattaunawa a cikin matsin lamba.

A hudubarsa ta farko Hujjatul-Islam Wal Muslimin Abu Turabi ya yi magana akan ranakun shahadar Sayyidah Fatimah ‘yar ma’aikin Allah (a.s) tare da bayyana matsayinta na cewa; Allah yana fushi da fushinta, yana kuma yarda da yardarta.

Hujjatul-Islam Abu Turabi ya ce, babu yadda za a yi ace Fatima ta yi fushi, ba a sami fushin Allah a wurin ba, haka nan kuma babu inda za ta yarda da wani abu, ba tare da an sami yardar Allah a tare da wannan abin ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments